20 Darajata garau take a gare ni, Bakana kullum sabo yake a hannuna.
20 Ɗaukakata za tă kasance tare da ni garau, bakana koyaushe sabo ne a hannuna.’
Duk da haka bakunansu sun kakkarye. Damatsansu sun yayyage Ta wurin ikon Allah Mai Girma na Yakubu, Makiyayi, Dutse na Isra'ila.
Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimako Za su ji an sabunta ƙarfinsu. Za su tashi da fikafikai kamar gaggafa, Sa'ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba, Sa'ad da suke tafiya, ba za su ji kasala ba.
Saboda haka ba mu karai ba, ko da yake jikinmu na mutuntaka yana ta lalacewa, duk da haka, ruhunmu a kowace rana sabunta shi ake yi.
Ya cika raina da kyawawan abubuwa, Don in zauna gagau, Ƙaƙƙarfa kamar gaggafa.
Yakan horar da ni don yaƙi, Domin in iya amfani da baka mafi ƙarfi.
Amma kai, ya Ubangiji, kullum kana kiyaye ni daga hatsari, Kana ba ni nasara, Kana kuma maido mini da ƙarfin halina.
Ku faɗa wa mahaifina dukan darajar da nake da ita a Masar da dukan abin da kuka gani. Ku gaggauta ku gangaro mini da mahaifina a nan.”
Adalci shi ne suturata, Gaskiya ita ce rigata da rawanina.
Gama ya kwashe dukiyata duka, Ya ɓata mini suna.