6 Akwai duwatsu masu daraja cikin duwatsunta, Akwai zinariya a ƙurarta.
6 akwai duwatsu masu daraja a cikin duwatsunta, akwai kuma zinariya a cikin ƙurarta.
Ko zinariyar Ofir, ko onis, Ko saffir, wato duwatsu masu daraja, ba za su iya biyan tamaninta ba.
Suka ga Allah na Isra'ila. Wurin da yake ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yakutu, garau kamar sararin sama.
An kuma ƙawata harsasan garun birnin da kowane irin dutse mai daraja. Yasfa shi ne na farko, na biyu saffir, na uku agat, na huɗu zumurrudu,
Ubangiji ya ce, “Ya Urushalima, mai shan wahala, birnin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi, Ba ki da wanda zai ta'azantar da ke. Zan sake gina harsashinki da duwatsu masu daraja.
Hannuwansa kyawawa ne, Saye da ƙawanen da aka yi musu ado da duwatsu masu daraja. Ƙugu nasa sumul sumul ne kamar hauren giwa da aka manne da yakutu.
“Daga cikin ƙasa ake samun abinci, Amma a ƙarƙashinta yakan zama kamar wuta.
Tsuntsu mai cin nama bai san wannan hanya ba. Shaho ma bai gan ta ba.