27 Shi ya san hikimar, shi ya sanar, Ya tabbatar da ita, ya bincike ta sarai.
27 sai ya dubi hikima ya auna ta; ya tabbatar da ita, ya gwada ta.
Dubi yadda sararin sama yake bayyana ɗaukakar Allah! Dubi yadda suke bayyana a fili ayyukansa da ya yi!
Sa'ad da ya ba da umarni ga ruwan sama, Da kuma hanyar da tsawa za ta bi,
“Allah ya ce wa mutane, ‘Duba, tsoron Ubangiji shi ne hikima, Rabuwa da mugunta kuma, ita ce haziƙanci.’ ”