Ku roƙi ruwan sama daga wurin Ubangiji a lokacin bazara, Gama Ubangiji ne yake yin gizagizan hadiri, Shi ne yake bai wa mutane yayyafi. Shi ne kuma yake ba kowane mutum tsire-tsiren saura.
Na hana wa shuke-shukenku ruwa A lokacin da suka fi bukata. Na sa a yi ruwa a wani birni, A wani birni kuwa na hana, Wata gonar ta sami ruwan sama, Amma wadda ba ta samu ba ta bushe.
A cikin gumakan al'ummai akwai mai iya sa a yi ruwa? Sammai kuma su yi yayyafi? Ashe, ba kai ne ba, ya Ubangiji Allahnmu? Domin haka a gare ka muke sa zuciya, Gama kai ne mai yin waɗannan abubuwa duka.”