25 Sa'ad da Allah ya sa iska ta hura, Ya yi wa tekuna iyaka.
25 Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura, ya kuma auna ruwaye.
Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya, Yakan yi walƙiya domin hadura, Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.
Akwai wanda zai iya auna teku da tafin hannu, Ko sararin sama da tafin hannunsa? Akwai wanda zai iya tallabe turɓayar duniya a cikin finjali, Ko ya iya auna duwatsu da tuddai a ma'auni?
Akan yi fari sa'ad da Allah ya hana ruwan sama, Rigyawa takan zo sa'ad da ya kwararo ruwa.
“Wa ya yi wa teku iyaka Sa'ad da ta tumbatso daga zurfafa?
Koka san yadda Allah yakan ba su umarni, Ya sa walƙiyar girgijensa ta haskaka?
A ina kake sa'ad da na aza harsashin gina duniya? Faɗa mini idan ka sani.
Wane ne ya zayyana kusurwoyinta? Hakika ka sani. Wane ne kuma ya auna ta?