20 “To, daga ina hikima ta fito? A wane wuri kuma haziƙanci yake?
20 “To, daga ina ke nan hikima ta fito? Ina fahimta take zama?
In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.
Amma ina, a ina za a iya samun hikima? A ina za a samo haziƙanci?
Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
“Allah ya ce wa mutane, ‘Duba, tsoron Ubangiji shi ne hikima, Rabuwa da mugunta kuma, ita ce haziƙanci.’ ”
“Allah ne kaɗai ya san hanya zuwa gare ta, Ya san inda hikima take,
Ubangiji ne yake ba da hikima. Ilimi da fahimi kuwa suna cikin kalmominsa.
Ba talikin da ya iya ganinta, Ko tsuntsun da yake tashi sama.