Ayuba 28:2 - Littafi Mai Tsarki2 Mutane sukan haƙo baƙin ƙarfe daga ƙasa, Sukan narkar da tagulla daga dutse. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Daga cikin ƙasa ake ciro ƙarfe, ana kuma narkar da tagulla daga cikin dutse. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da wahala mai yawa na yi tanadi domin Haikalin Ubangiji, zinariya wajen talanti dubu ɗari (100,000), da azurfa kuma wajen talanti zambar dubu (1,000,000), domin gina Haikalin Ubangiji. Bayan wannan akwai tagulla da ƙarfe masu tarin yawa. Na kuma tanada katakai da duwatsu. Kai kuma sai ka ƙara a kansu.