Amma ina kama da lafiyayyen ɗan rago, Wanda aka ja zuwa mayanka, Ashe, ni suke ƙulla wa munafuncin! Ni kuwa ban sani ba, da suke cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da 'ya'yansa. Bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, Har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.”
“Elam tana can da dukan jama'arta kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Sun gangara da rashin imaninsu zuwa lahira. Su ne suka haddasa tsoro a duniya. Sun sha kunyarsu tare da waɗanda suka gangara zuwa kabari.