Ko da sun yi azumi, ba zan ji kukansu ba, ko da sun miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta sha, ba zan karɓe su ba. Amma zan hallaka su da takobi, da yunwa, da annoba.”
“Sa'ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu'a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu'ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.
In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe ƙofa, kun kuma fara tsayawa daga waje, kuna ƙwanƙwasa ƙofar, kuna cewa, ‘Ya Ubangiji, buɗe mana,’ sai ya amsa muku ya ce, ‘Ku kam, ban san daga inda kuke ba.’