3 Muddin ina numfashi, Ruhun Allah kuma yana cikin hancina
3 Muddin ina da rai a cikina kuma numfashin Allah yana cikin hancina,
Sa'an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.
Ruhun Allah ne ya yi ni, Mai Iko Dukka ya hura mini rai.
Kada ku dogara ga 'yan adam. Wace daraja take gare su?
Amma Ruhun Allah Mai Iko Dukka ne wanda yake cikin mutum, Yakan ba mutane basira.
Haka kuma ba ya neman wani taimako gun mutum, sai ka ce wani abu yake bukata, tun da yake shi kansa ne yake ba dukkan mutane rai, da numfashi, da dukkan abubuwa.
Allah shi ne yake bi da rayukan talikansa. Numfashin dukan mutane kuwa a ikonsa yake.