Dukan masu wucewa suna yin miki tafin raini. Suna yi wa Urushalima tsāki, Suna kaɗa mata kai, suna cewa, “Ai, Urushalima ke nan, Birnin nan da ake cewa mai cikakken jamali, Wanda ya ƙayatar da dukan duniya?”
Wannan shi ne birnin da yake da harka, mai zaman lafiya, Wanda yake ce wa kansa, “Ba wani sai ni.” Ga shi, ya zama kufai, Wurin zaman dabbobi! Duk wanda ya wuce ta wurin, Zai yi tsaki, ya kaɗa kai.
Wannan Haikali kuwa zai zama tsibin juji, duk wanda zai wuce ta wurin, zai yi mamaki, ya yi tsaki, ya ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi wa ƙasar nan da Haikalin nan haka?’
Domin kun kiyaye dokokin Omri, Kun bi halin gidan Ahab, Kun kuma bi shawarwarinsu. Domin haka zan maishe ku kufai, In mai da ku abin dariya, Za ku sha raini a wurin mutanena.”