18 Sun gina gidajensu kamar saƙar gizo-gizo, Kamar bukkar mai tsaro.
18 Gidan da ya gina kamar gidan gizo-gizo, kamar bukkar mai tsaro.
Urushalima kaɗai ta ragu, birnin da aka kewaye da yaƙi, ba wata kariya kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, ko ta mai ƙumu a gonar kankana.
Irin waɗannan mutane za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye! Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada, Nasarata za ta kasance har abada abadin.”
Ya rushe Haikalinsa kamar bukka cikin gona, Ya mai da wurin yin ƙayyadaddun idodinsa kufai. Ubangiji ya sa ƙayyadadden idi da kiyaye Asabar Su ƙare a Sihiyona, Da zafin fushinsa kuma ya wofinta sarki da firist.
An datse raina, ya ƙare, Kamar alfarwar da aka kwance, Kamar saƙar da aka yanke, Na zaci Allah zai kashe ni.
Dā yana zaune lafiya, Sai razana ta tatike shi, Ta jawo shi zuwa ga Sarkin Mutuwa.