“Ai, waɗannan duka za su yi ta yi masa zambo, Su yi masa dariya ta raini, Su ce, ‘Tasa ta ƙare, shi wanda ya tattara abin da ba nasa ba, Har yaushe zai riƙa arzuta kansa ta hanyar ba da rance?’
Allah ne yake ba da hikima, da ilimi, da farin ciki ga wanda yake ƙauna. Amma yakan sa matalauci, mai zunubi, ya yi ta wahalar nema ya tara dukiya, domin Allah ya bayar ga wanda yake ƙauna. Wannan ma aikin banza ne, harbin iska ne kawai.
A wannan rana sai sarki Ahasurus ya ba Esta gidan Haman, maƙiyin Yahudawa, da duk dukiyar Haman. Mordekai kuwa ya zo gaban sarki, gama Esta ta bayyana yadda yake a gare ta.