12 Ga shi kuwa, dukanku kun gani da kanku, Me ya sa kuka zama wawaye?
12 Duk kun ga wannan ku da kanku saboda haka me ya sa kuke maganganun nan marasa ma’ana?
Dubi aikin banza da yake faruwa a duniya. Wani lokaci adalai suke shan hukuncin da za a yi wa mugaye, mugaye kuwa su karɓi sakayyar da za a ba adalai. Na ce wannan ma aikin banza ne.
Ku ba ni zarafi in yi magana, sa'an nan in na gama ku amsa in kun ga dama.
Na lura da yadda mutane suke yi mini mummunar ba'a.
Ka dinga yin magana ke nan har abada? A kullum maganarka ita ce dahir?
“Zan koya muku zancen ikon Allah, Abin da yake na wajen Mai Iko Dukka ba zan ɓoye ba.
“Wannan shi ne rabon mugaye daga wurin Allah, Gādo ne kuma wanda azzalumai za su karɓa daga wurin Mai Iko Dukka.