Wa ya taɓa hawa cikin Sama ya sauko? Wa ya taɓa kama iska cikin tafin hannunsa? Wa ya taɓa ƙunshe ruwa cikin rigarsa? Wa kuma ya kafa iyakar duniya? Ina sunansa, ina kuma sunan ɗansa? Hakika ka sani!
Sa'ad da ya yi murya akan ji ƙugin ruwa a cikin sammai Yakan kawo ƙasashi daga ƙurewar duniya, Yakan yi walƙiyoyi saboda ruwan sama, Daga cikin taskokinsa yakan kawo iska.
Zan bar ciyayi su rufe ta. Ba zan yi wa kurangar inabin aski ba, ko in yi mata noma, amma zan bar sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa su rufe ta. Har ma zan sa gizagizai su hana ta ruwan sama.”