6 Lahira tsirara take a gaban Allah, Haka kuma Halaka take a gaban Allah.
6 Mutuwa tsirara take a gaban Allah; haka kuma hallaka take a buɗe.
Ko lahira ba za ta hana Ubangiji ya san abin da yake can ba. Ƙaƙa fa mutum zai iya ɓoye wa Allah tunaninsa?
Idan na hau cikin samaniya kana can, In na kwanta a lahira kana can,
Ko da za su nutsa zuwa lahira, Zan kama su. Ko sun hau Sama, Zan turo su.
Halaka da Mutuwa sun ce, ‘Da kunnuwanmu mun ji ƙishin-ƙishin a kanta.’
Ba wata halittar da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili yake, a shanye sosai a gaban idon wannan da za mu ba da lissafi a gabansa.
“Lahira tana shirye-shiryen yi wa Sarkin Babila maraba. Fatalwan waɗanda suka yi iko a duniya suna kaiwa suna komowa a hargitse. Fatalwan sarakuna suna tashi daga gadajen sarautarsu.
Da na iya roƙon duhu ya ɓoye ni, Ko haske da yake kewaye da ni Ya zama dare,
Kakan yi wa matattu mu'ujizai ne? Sukan tashi su yabe ka?
Wa ya ba ni har da zan biya shi? Dukan abin da yake cikin duniyan nan nawa ne.
Sararin sama ba shi ne matuƙa a wurin Allah ba, Amma ga shi, yana can nesa da kai, Allah ya san lahira, Amma kai ba ka sani ba.
Sarkinsu kuwa da yake iko da su shi ne mala'ikan mahallaka, sunansa da Yahudanci Abadan, da Helenanci kuwa Afoliyon.
Da a ce na mutu a lokacin, da yanzu ina huce,
Yakan kawar da manyan duwatsu farat ɗaya, Ya hallaka su da fushinsa,
Za ta zama wuta mai ci har ta hallaka, Za ta cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.
An taɓa nuna maka ƙofofin mutuwa? Ko kuwa ka taɓa ganin ƙofofin duhu ƙirin?
Muradin mutum kamar lahira yake, a kullum ba ya ƙoshi.
Yana bayyana zurfafan abubuwa masu wuyar ganewa, Ya san abin da yake cikin duhu. Haske kuma yana zaune tare da shi.