Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura, Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki. Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki, Ya ɗora su a wurare masu maƙami. Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne, A kansu ya kafa duniya.
Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar ɓarawo, sa'an nan sammai za su shuɗe da ƙara mai tsanani, dukkan abin da yake a cikinsu za su ƙone, su hallaka, ƙasa kuma da abubuwan da suke a kanta, duk za su ɓăce.