“Kamar yadda ɓarawo yakan sha kunya sa'ad da aka kama shi, Haka nan mutanen Isra'ila za su sha kunya, Da su, da sarakunansu, da shugabanninsu, Da firistocinsu, da annabawansu.
Za ta yi ta auko muku a kai a kai kowace safiya. Tilas ku sha ta dare da rana. Kowane sabon jawabin da zai zo muku daga wurin Allah, zai kawo muku sabuwar razana!