5 Ina so in san irin amsar da zai mayar mini, Ina kuma so in san yadda zai amsa mini.
5 Zan nemi in san abin da zai ce mini, in kuma auna abin da zai ce mini.
Kada ka hukunta ni, ya Allah. Ka faɗa mini laifin da kake tuhumata da shi.
Da zan kai ƙarata a gare shi, in faɗa masa duk muhawarata, in kāre kaina ne.
Allah kuwa da dukan ƙarfinsa zai yi gāba da ni? A'a, zai saurara in na yi magana.