ya ce musu, ‘Ku ji, ya ku Isra'ilawa, yau kuna gab da kama yaƙi da magabtanku, kada ku karai, ko ku ji tsoro, ko ku yi rawar jiki, ko ku firgita saboda su.
Sai na ce, “Sa zuciyata ya ƙare! Na shiga uku! Kowace maganar da ta fito bakina zunubi ce, ina zaune a tsakanin mutane waɗanda duk maganarsu zunubi ce, ba ta da tsarki. Amma yanzu da idona na ga Sarki, Ubangiji Mai Runduna!”
Kada zuciyarku ta yi suwu, Kada kuma ku ji tsoro saboda labarin da ake ji a ƙasar, Labari na wannan shekara dabam, na wancan kuma dabam, A kan hargitsin da yake a ƙasar, Mai mulki ya tasar wa mai mulki.