Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayuba 23:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Duk da haka Allah ya san kowane irin hali da nake ciki. Idan ya jarraba ni zai tarar ni tsattsarka ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Amma ya san hanyar da nake bi; sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayuba 23:10
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Albarka tā tabbata ga mai jimirin gwaji, domin in ya jure gwajin, sai ya sami kambin rai, wanda Ubangiji ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari.


Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta), domin bangaskiyar nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu.


Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta, Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa, Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya. Za su kira gare ni, Zan kuwa amsa musu, Zan ce, ‘Su jama'ata ne,’ Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”


Ka jarraba mu, ya Allah, Kamar yadda ake tace azurfa da wuta, Haka nan ka jarraba mu.


Zinariya da azurfa da wuta ake gwada su, zuciyar ɗan adam kuwa Ubangiji ne yake gwada ta.


Ka san zuciyata, Kakan zo gare ni da dare, Ka riga ka jarraba ni sarai, Ba ka kuwa sami mugun nufi a cikina ba. Na ƙudurta kuma bakina ba zai yi saɓo ba.


Ta wurin bangaskiya Ibrahim, sa'ad da aka gwada shi, ya miƙa Ishaku hadaya, wato shi da ya yi na'am da alkawaran nan, ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa,


Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”


Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina.


Gama Ubangiji yana lura da al'amuran adalai, Amma al'amuran mugaye za su watse.


Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.


“Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya, na aikata abin da yake mai kyau a gabanka.” Sai ya yi ta rusa kuka.


Gama na zaɓe shi don ya umarci 'ya'yansa da gidansa domin su kiyaye tafarkin Ubangiji a bayansa, su riƙe adalci da shari'a.” Ubangiji ya tabbatar wa Ibrahim da abin da ya alkawarta masa.


In kuwa aikin wani ya ƙone, to, sai yă yi hasara, ko da yake shi da kansa zai tsira, amma kamar ya bi ta wuta ne.


Kai, kun zaƙe, ku daina aikata rashin adalci, Kada ku sa mini laifi, nake da gaskiya.


Kakan dube shi kowace safiya. Kana jarraba shi a kowane daƙiƙa.


Ina da aminci, zan faɗa wa Allah ra'ayina, Zai tabbatar da amincina duka.


Allah ya tafi wurin aiki a dama, Ya kuma tafi hagu, amma har yanzu ban gan shi ba.


Bari Allah ya auna ni da ma'aunin da yake daidai, Zai kuwa san mutuncina.


Ka tsai da muguntar mugaye, Ina roƙonka, ka sāka wa mutanen kirki. Kai Allah mai adalci ne, Kana kuwa auna tunanin mutane, da marmarinsu.


Yana auna masu kirki da mugaye dukka, Yana ƙin marar bin doka gaba ɗaya.


Gama na kiyaye dokar Ubangiji, Ban yi wa Allahna tayarwa ba.


Ka sani, ba ni da laifi, Ka kuma sani, ba wanda zai cece ni daga gare ka.


Allah ya san dukan abin da nake yi, Yana ƙididdige dukan takawata.


Ka ce kai tsattsarka ne, ba ka da laifi, Kai tsabtatacce ne, ba ka da wata ƙazanta.


Amma kai, ya Ubangiji, kana sane da ni, kana ganina, Kai kanka kake gwada tunanina. Ka jawo su kamar tumaki zuwa mayanka, Ka ware su domin ranar yanka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ