8 Ka mori ikonka da matsayinka, Don ka mallaki dukan ƙasar.
8 Ko da yake kai mai ƙarfi ne, ka mallaki ƙasa, mutum mai martaba kuma, kana zama cikin ƙasarka.
wato tsofaffi da manyan mutane su ne kawunan, ƙafafu kuwa su ne annabawan da suke koyar da ƙarairayi!
Sun himmantu su aikata abin da yake mugu da hannuwansu. Sarki da alƙali suna nema a ba su hanci, Babban mutum kuma yana faɗar son zuciyarsa, Da haka sukan karkatar da zance.
da shugabannin sojojinsu, da na farar hula, da 'yan siyasarsu, da kowane mai aikin sihiri don ya sarrafa abubuwan da yake faruwa.
Akwai mugaye ko'ina, suna ta yanga, Suna ta yabon abin da yake mugunta.
Ko na tsaya shiru saboda tsoron taron jama'a, Saboda kuma baƙar maganar mutane ta razanar da ni.
Son zuciya kuke yi, ko ba haka ba? Kuna goyon bayan Allah? Za ku goyi bayan Allah sa'ad da aka gurfanar da ni gaban shari'a?
Allah ya ba da duniya ga mugaye, Ya makantar da dukan alƙalai, Idan ba Allah ne ya yi haka nan ba, to, wa ya yi?
Yakan ƙasƙantar da firistoci da mutane masu iko.