“Ku bi titunan Urushalima ko'ina! Ku dudduba ku lura! Ku bincika kowane dandali, ku gani, Ko za ku iya samun ko mutum ɗaya Mai aikata adalci, mai son gaskiya, Sai in gafarta mata.
Za ku sāke gina tsofaffin kufanku na dā can, za ku sāke kafa tushen zuriya da yawa. Za a kira ku, ‘Masu gyaran abin da ya lalace, masu sāke gyaran gidaje.’ ”
“Sa'ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu'a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu'ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.
Sai Elifaz mutumin Teman, da Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na'ama suka tafi suka yi kamar yadda Ubangiji ya faɗa musu, Ubangiji kuwa ya karɓi addu'ar Ayuba.