Sa'an nan za ku yi kira, ni kuwa zan amsa, za ku yi kuka, ni kuwa zan ce muku, ‘Ga ni.’ “Idan kuka kawar da karkiya daga cikinku, kuka daina nuna wa juna yatsa, da faɗar mugayen maganganu,
“Idan kun yi wa Ubangiji Allahnku wa'adi, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama Ubangiji Allahnku zai neme shi a gare ku, ba kuwa zai zama zunubi a gare ku ba.
Yabez ya roƙi Allah na Isra'ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.
Sa'ad da ya yi addu'a gare shi, Allah ya karɓi roƙonsa da hurwarsa, ya sāke komar da shi Urushalima da mulkinsa. Sa'an nan ne Manassa ya sani Ubangiji shi ne Allah.