20 Duk abin da mugu ya mallaka ya hallaka, Wuta kuwa ta lashe kowane abu da ya ragu.
20 ‘Ba shakka an hallaka maƙiyanmu, wuta kuma ta ƙona dukiyarsu.’
Aka hallaka dukan abin da ya tattara, Wutar da ba hannun mutum ya kunna ba Ta ƙone shi, shi da iyalinsa duka.
Kafin yă gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Tsawa ta kashe tumaki da makiyayansu duka, ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”
Ba kuwa zai kuɓuta daga duhu ba. Zai zama kamar itacen da wuta ta ƙone rassansa, Kamar itace kuma da iska ta kaɗe furensa.
“Yanzu fa sai ka yi tunani. Ka faɗi bala'i ɗaya wanda ya taɓa fāɗa wa adalin mutum.
Sai Ubangiji ya yi ta zuba wa Saduma da Gwamrata wutar kibritu daga sama,
Ba ga shi ma, sai kamar baƙi yake ɗaukarmu ba? Gama ya sayar da mu, yana kuwa morar kuɗin da aka bayar dominmu.
“Wannan ita ce ƙaddarar mugaye, Wadda Allah ya ƙayyade musu.”