In idonka na dama yana sa ka yi laifi, to, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa duk jikinka ɗungum a Gidan Wuta.
Haka kuma ba ya neman wani taimako gun mutum, sai ka ce wani abu yake bukata, tun da yake shi kansa ne yake ba dukkan mutane rai, da numfashi, da dukkan abubuwa.