17 Su ne mutanen da suka ƙi Allah, Suka kuwa gaskata ba shi da ikon yi musu kome,
17 Suka ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu! Me Maɗaukaki zai yi mana?’
Akwai mutane da yawa da suke cewa, “Da ma a sa mana albarka!” Ka dube mu da alheri, ya Ubangiji!
Tun da yake sun ƙi su yarda su san Allah, Allah ya sallama su ga halin banza, su aikata abin kunya.
Sai ga duk jama'ar garin sun firfito su taryi Yesu. Da suka gan shi, sai suka roƙe shi ya bar musu ƙasarsu.
Sai suka ƙwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai Ɗan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?”
Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Ubangiji. Ina amfani a kiyaye abin da ya ce, ko mu yi ƙoƙarin nuna cewa zuciyarmu ta ɓāci saboda ayyukan da muka yi wa Ubangiji Mai Runduna.
Tashi daga nan, kada ku toshe mana hanya. Ba ma so mu ji kome game da Allah Mai Tsarki na Isra'ila.”
Hakika shanunsu suna ta hayayyafa, Suna haihuwa ba wahala.
Gama tun da na tafi wurin Fir'auna, na yi masa magana da sunanka, ya mugunta wa wannan jama'a, kai kuwa ba ka ceci jama'arka ba ko kaɗan!”