tun da yake bai rangwanta wa mutanen tun can dā dā kuma ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa'azin adalci, da waɗansu mutum bakwai, sa'ad da ya aiko da Ruwan Tsufana zuwa a cikin duniyar nan ta marasa bin Allah,
A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.
Amma kai, ya Allah, za ka jefar da masu kisankai, da maƙaryata can ƙasa cikin zurfafa, Kafin su kai rabin kwanakinsu a duniya. Amma ni, zan dogara gare ka.
Ubangiji yana da wani ƙaƙƙarfa mai iko a shirye don ya fāɗa musu da yaƙi. Zai zo kamar hadirin ƙanƙara, kamar kwararowar ruwan sama, kamar kuma rigyawa mai kirmewa wadda ta shafe ƙasa.