11 An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani, Rigyawa ta sha kanka.
11 An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani, shi ya sa ambaliyar ruwa ta rufe ka.
Ruwa ya sha kaina, Sai na ce, ‘Na halaka.’
Ka jefa ni cikin zurfi, Can cikin tsakiyar teku, Inda igiyoyin ruwa suka kewaye ni, Kumfa da raƙuman ruwanka suka bi ta kaina.
Allah ya rufe hanya, na kasa wucewa, Ya rufe hanyata da duhu,
'ya'yan Mulki kuwa sai a jefa su matsanancin duhu. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.”
Ya kore ni zuwa cikin duhu baƙi ƙirin.
ko su zura wa ƙasa ido, amma ba abin da za su gani, sai wahala da duhu mai banrazana, inda za a kora su a ciki.
Hanyar mugaye kuwa duhu ne baƙi ƙirin, kamar duhun dare. Sukan fāɗi, amma ba su san abin da ya sa suka yi tuntuɓe ba.
Zurfafan tekuna suna kiran junansu, Matsirgar ruwa na Allah kuwa suna ta ruri! Igiyoyin ruwa na baƙin ciki Suka yi wa raina ambaliya.
“Kana iya yi wa gizagizai tsawa, Don su kwararo ruwan sama, ya rufe ka?
Za a kore shi daga ƙasar masu rai, Za a kore shi daga haske zuwa duhu.
Fitilar da take cikin alfarwarsa ba za ta ba da haske ba.
Da rana sukan yi karo da duhu, Ko da tsakar rana ma lalube suke kamar ana duhu.
Duk wahalarka za ta gushe daga tunaninka, Kamar yadda rigyawa takan wuce, ba a ƙara tunawa da ita.
“Rigyawa takan ci mugun mutum, Ƙasar da ya mallaka kuwa tana ƙarƙashin la'anar Allah. Ba ya kuma iya zuwa aiki a gonar inabinsa.