Kai mai tsarki ne, Ka fi ƙarfin ka dubi mugunta. Kai da ba ka duban laifi. Me ya sa kake duban marasa imani? Kana iya shiru sa'ad da mugu yake haɗiye Mutumin da ya fi shi adalci?
Wannan shi ne hukuncin da tsarkaka, Masu tsaro suka shawarta, Suka yanke domin masu rai su sani Maɗaukaki yake sarautar 'yan adam, Yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama, Yakan sa talaka ya zama sarki.’
Dubi aikin banza da yake faruwa a duniya. Wani lokaci adalai suke shan hukuncin da za a yi wa mugaye, mugaye kuwa su karɓi sakayyar da za a ba adalai. Na ce wannan ma aikin banza ne.