Suka ce masa, “Yi mana shiru, kame bakinka. Ka biyo mu, ka zama firist namu da mai ba mu shawara. Bai fi kyau ka zama firist na kabilar Isra'ila ba, da a ce ka zama na gidan mutum guda kawai?”
Suka hango Ayuba tun daga nesa, amma ba su gane shi ba. Da suka gane shi sai suka fara kuka da murya mai ƙarfi. Suka kyakkece tufafinsu saboda baƙin ciki, suka ɗibi ƙura suka watsa a kawunansu.
Amma yanzu al'ummai da yawa za su yi mamaki a kansa, Sarakuna kuwa za su riƙe baki saboda mamaki. Za su gani su kuma fahimci abin da ba su taɓa sani ba.”