4 “Ba da 'yan adam nake faɗa ba, Ina da isasshen hanzarin da zai sa in yi fushi.
4 “A wurin mutum ne na kawo kukana? Don me ba zan kāsa haƙuri ba?
Me ya sa ni ɓacin rai haka? Me ya sa ni damuwa? Zan dogara ga Allah. Har yanzu ma zan yabe shi, Mai Cetona, Allahna.
Sai ya ce musu, “Raina yana shan wahala matuƙa, har ma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a faɗake tare da ni.”
Ka ji addu'ata, ya Ubangiji, Ka ji kukana na neman taimako!
Wane ƙarfi ne nake da shi na rayuwa? Wane sa zuciya kuma nake da ita, tun da na tabbata mutuwa zan yi?
Kada ka zaci ni 'yar iska ce. Ni dai ina faɗar damuwata da tsokanar da ake yi mini ne.”
Sai Musa ya faɗa wa Isra'ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne gare shi ba, saboda ɓacin rai da tsananin bauta.
In haka ne, me ya sa kake bin diddigin dukan laifofina, Kana farautar dukan abin da na yi?