32 Sa'ad da aka ɗauke shi zuwa hurumi, A inda ake tsaron kabarinsa,
32 Za a bizne shi a kabari, a kuma yi tsaron kabarinsa.
Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, mala'iku kuma suka ɗauke shi, suka kai shi wurin Ibraham. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.
Za a ƙaddara su ga mutuwa kamar tumaki, Mutuwa ce za ta yi kiwonsu. Da safe adalai za su ci nasara a kansu, Sa'ad da gawawwakinsu suke ruɓewa a ƙasar matattu, Nesa da gidajensu.
Ba wanda zai fito fili ya zargi mugun, Ko ya mayar masa da martani.
Dubban mutane sukan tafi wurin jana'izarsa, Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali.
Amma za ku mutu kamar kowane mutum, Ku fāɗi kamar kowane basarauce.”