Bulus yana ba da bayani a kan adalci, da kamunkai, da kuma hukuncin nan mai zuwa, Filikus ya kaɗu, ya kāda baki ya ce, “Yanzu kam, sai ka koma. In na sami zarafi nā kira ka.”
Kun aikata waɗannan duka, ni kuwa ban ce kome ba, Saboda haka kuka zaci ni kamar ku nake. Amma yanzu zan tsauta muku, In bayyana muku al'amarin a fili.
“Kukan ce Allah yakan hukunta yaro saboda zunuban mahaifinsa. A'a! Allah dai yakan hukunta wa masu zunubi. Ya kuma nuna ya yi haka saboda zunubansu ne.