21 Bayan rasuwar mutum, Ruwansa ne ya sani ko 'ya'yansa suna jin daɗi?
21 Ko zai damu da iyalin da ya bari a baya sa’ad da kwanakinsa suka ƙare?
Tsawon kwanakin ransa, an ƙayyade su tun can, An ƙayyade yawan watannin da zai yi, Ka riga ka yanke haka ya Allah, ba su sākuwa.
Ya Allahna, kada ka ɗauke ni a yanzu, Tun da yake ban tsufa ba tukuna! Ya Ubangiji har abada kake.
Amma kai, ya Allah, za ka jefar da masu kisankai, da maƙaryata can ƙasa cikin zurfafa, Kafin su kai rabin kwanakinsu a duniya. Amma ni, zan dogara gare ka.
'Ya'yansa maza za su sami girma, amma sam, ba zai sani ba, Sam, ba wanda zai faɗa masa sa'ad da aka kunyatar da su.
Bari dai a hukunta masu zunubi Su kuma ga hasalar Allah.
Mutum zai iya koya wa Allah? Mutum zai iya shara'anta wa Allah Mai Iko Dukka?