zai ci karo da azabar Allah tsantsa ta tsananin fushinsa, za a kuwa azabta shi da wuta, da duwatsun wuta, a gaban mala'iku tsarkaka, da kuma Ɗan Ragon.
Ya Urushalima, ki farka! Ki tashi da kanki, ki miƙe! Kika sha ƙoƙon hukunci wanda Ubangiji, cikin fushinsa, ya ba ki ki sha, Kika shanye shi, ya kuwa sa ki yi tangaɗi!
Daga cikin bakinsa wani kakkaifan takobi yake fitowa, wanda zai sare al'ummai da shi, zai kuwa mallake su da tsanani ƙwarai, zai tattake mamatsar inabi, ta tsananin fushin Allah Maɗaukaki.