12 Suna rawa ana kaɗa garaya, Ana busa sarewa.
12 Suna rera da kayan kiɗa na ganga da garaya; suna jin daɗin busar sarewa.
A cikin bukukuwanku kuna kaɗa garaya, da bandiri, da bushe-bushe, da ruwan inabi. Amma ba ku gane da abin da Ubangiji yake yi ba.
Sunan ɗan'uwansa Yubal, wanda ya zama uban makaɗan garaya da mabusan sarewa.
A maimakon haka sai kuka yi dariya, kuka yi biki. Kuka yanka tumaki da shanu don ku ci, kuka sha ruwan inabi. Kuka ce, “Gara mu ci mu sha! Gobe za mu mutu.”
Me ya sa ka gudu a ɓoye? Ka cuce ni, ba ka kuwa faɗa mini ba, ai, da na sallame ka da farin ciki, da waƙe-waƙe, da kiɗa, da garaya.
'Ya'yansu suna guje-guje, Suna tsalle kamar 'yan raguna,
Suka yi zamansu da salama, Su mutu shiru ba tare da shan wahala ba.
Ku yabe shi da bandiri kuna taka rawa! Ku yabe shi da garayu da sarewa!