5 Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.
5 mugun mutum bai taɓa daɗewa ba, farin cikin mutum na ɗan gajeren lokaci ne.
Amma ga shi, kuna fariya ta alfarmar banza da kuke yi. Duk irin wannan fariya kuwa muguwar aba ce.
Kowa yă auna aikinsa ya gani, sa'an nan ne zai iya gadara da maƙaminsa shi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.
“Ba duk mai ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji,’ ne zai shiga Mulkin Sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so.
Wace sa zuciya take ga marar tsoron Allah? Sa'ad da Allah ya datse shi, ya ɗauke ransa?
Hakika matuƙar murnar da mugaye suke da ita ke nan, Yanzu waɗansu ne za su zo su gāje wurarensu.
Na ga waɗansu wawaye waɗanda ake gani kamar suna zaune lafiya, Amma nan da nan sai na la'anci gidajensu.
Aka kuwa rataye Haman a gungumen itace da ya shirya zai rataye Mordekai. Sa'an nan sarki ya huce.
Bai kamata marar tsoron Allah ya yi mulki ba, Don kada ya tura jama'a cikin tarko.
Har yaushe mugaye za su yi ta murna? Har yaushe ne, ya Ubangiji?
Yowab ya ce, “Ba zan ɓata lokaci haka da kai ba.” Sai ya ɗibi mashi uku ya soki Absalom a ƙahon zuciya, tun yana da sauran rai, a maƙale cikin itacen oak.
Sa'an nan samari goma masu ɗaukar wa Yowab makamai, suka kewaye Absalom, suka yi ta dūkansa har ya mutu.
Kuna ta tambaya, ‘Ina ne gidan babban mutumin nan yanzu, Wato mutumin da yake aikata mugunta?’
A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe, Za ka neme su, amma ba za a same su ba,
Har yaushe za su yi shakiyanci, Su yi ta ɗaga kai? Har yaushe, ya Ubangiji?