4 “Hakika ka sani tun daga zamanin dā, Sa'ad da aka fara sa mutum a duniya,
4 “Ba shakka ka san yadda abin yake tuntuni, tun da aka sa mutum cikin duniya,
Samaniya ta Ubangiji ce kaɗai, Amma ya ba mutane duniya.
Na ce wa kaina, ‘Ya kamata kwanaki su yi magana, Yawan shekaru kuma su koyar da hikima.’
Daga wurin mutanen da suka yi furfura muka koyi hikimarmu. Mun koyi hikimarmu daga mutane waɗanda aka haife su Tun kafin a haifi mahaifinka.
Allah kuwa ya sa musu albarka, ya ce musu, “Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita, ku mallaki kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma dukan abin da yake da rai da yake kai da kawowa cikin duniya.”
Mutane masu hikima sun koya mini gaskiya Wadda suka koya daga wurin kakanninsu, Ba su kuwa ɓoye mini asirin kome ba.