“Kamar makwarwar da ta kwanta kan ƙwan da ba ita ta nasa ba, Haka yake ga wanda ya sami dukiyar haram, Yana gaɓar ƙarfinsa, za ta rabu da shi, A ƙarshe zai zama wawa.”
Kun shiga uku! Kuna ƙara wa kanku gidaje da gonaki a kan waɗanda kuke da su a dā. Ba da jimawa ba za a ga ba sauran filin da zai ragu ga kowa, ku kaɗai za ku zauna a ƙasar.
Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane suka cika gidajensu masu daraja da abubuwan da suka samo ta hanyar zamba, da ta kama-karya. Ta yadda za su yi su yi aminci ma, ba su sani ba.