Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayuba 2:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Suka hango Ayuba tun daga nesa, amma ba su gane shi ba. Da suka gane shi sai suka fara kuka da murya mai ƙarfi. Suka kyakkece tufafinsu saboda baƙin ciki, suka ɗibi ƙura suka watsa a kawunansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Sa’ad da suka gan shi daga nesa, da ƙyar suka gane shi; sai suka fara kuka da ƙarfi, suka yayyaga tufafinsu suka zuba toka a kawunansu,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayuba 2:12
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za su yi kuka mai zafi dominki. Za su yi hurwa, su yi birgima cikin toka.


Dattawan Sihiyona suna zaune a ƙasa shiru, Sun yi hurwa, suna saye da tufafin makoki. 'Yan matan Urushalima kuma sun sunkuyar da kansu ƙasa.


A rana ta ashirin da huɗu ga watan nan, sai jama'ar Isra'ila suka taru, suna azumi, suna saye da tufafin makoki, suna zuba toka a kansu.


Sai Ayuba ya tashi, ya kyakkece tufafinsa don baƙin ciki. Ya aske kansa, ya fāɗi ƙasa,


Sai Joshuwa ya yayyage tufafinsa, ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin Ubangiji har yamma. Shi da dattawan Isra'ila, suka zuba ƙura a bisa kansu.


Har suka tula wa kansu ƙasa suna ta kuka, suna baƙin ciki, suna kururuwa, suna cewa, “Kaito! Kaiton babban birnin nan! Wanda duk masu jiragen ruwa a bahar suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa, A sa'a ɗaya ya hallaka.


Da Mordekai ya ji dukan abin da aka yi, sai ya yage tufafinsa, sa'an nan ya sa rigar makoki, ya zuba toka a kā. Ya fita zuwa tsakiyar birni, yana ta rusa kuka da ƙarfi.


Yana gama magana ke nan, sai ga 'ya'yan sarki sun iso. Suka yi ta kuka da ƙarfi. Sarki kuma da dukan fādawansa suka yi kuka mai tsanani.


sai suka yi ta kuka da ƙarfi, har ƙarfinsu ya ƙare.


Da manzannin suka zo Gibeya inda Saul yake, suka ba mutane labarin abin da ya faru. Sai jama'a duka suka yi kuka.


Da mala'ikan Ubangiji ya faɗa wa Isra'ilawa wannan magana, suka yi kuka mai zafi.


Da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya yi kūwwa da kuka mai tsananin gaske, ya ce wa mahaifinsa, “Ka sa mini albarka, har da ni ma, ya babana.”


Wani mutumin kabilar Biliyaminu ya gudu daga dāgar yaƙin ya zo Shilo da tufafinsa ketattu ga kuma ƙura a kansa.


Sa'ad da na ji wannan, sai na yayyage rigata da alkyabbata, na tsittsiga gashin kaina da na gemuna, na zauna a ruɗe.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ