9 Gama ya kwashe dukiyata duka, Ya ɓata mini suna.
9 Ya cire darajar da nake da ita, ya kuma cire rawani daga kaina.
Ka ƙwace masa sandan sarautarsa, Ka buge gadon sarautarsa ƙasa.
Rawani ya fāɗi daga kanmu, Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!
Ka soke alkawarinka wanda ka yi wa bawanka, Ka jefar da kambinsa a cikin ƙazanta.
Darajar Ifraimu za ta tashi kamar tsuntsu, Ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki!
Amma za a sani, ku firistoci ne na Ubangiji, Za ku mori dukiyar al'ummai, Za ku yi fāriya da cewa, taku ce.
“Amma yanzu waɗanda na girme su, sai ba'a suke mini, Waɗanda iyayensu maza ba su fi karnukan da suke kiwon garken tumakina ba.
Yakan mai da hikimar masu mulki wauta, Yakan mai da shugabanni marasa tunani.
Yakan ƙasƙantar da firistoci da mutane masu iko.
“Ina makoki saye da tsummoki, Ina zaune cikin ƙura a kunyace.
domin dukiya ba ta tabbata har abada, al'ummai ma haka ne.
Ka rurrushe garun birninsa, Ka mai da sansaninsa mai kagara kufai.