“Saboda haka hanyarsu za ta zama da santsi da duhu, Inda za a runtume su, su fāɗi. Gama zai kawo musu masifa a shekarar da za su sha hukuncinsu.” Ubangiji ya faɗa.
Ku girmama Ubangiji Allahnku, Kafin ya kawo duhu, Kafin kuma ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan dutse, da duhu duhu, Sa'ad da kuke neman haske, sai ya maishe shi duhu, Ya maishe shi duhu baƙi ƙirin.
Ku duka da kuke tsoron Ubangiji, Kuna kuma biyayya da kalmomin bawansa, Zai yiwu hanyar da kuke bi ta yi duhu ƙwarai, Amma ku dogara ga Ubangiji, ku jingina ga Allahnku.
A sa'ad da suka yi mini kuka, na sa duhu a tsakaninsu da Masarawa, na sa teku ta shafe Masarawa. Da idonku kun ga abin da na yi wa Masar, kuka kuma zauna a jeji da daɗewa.
Mutane suna cewa, “Don haka ne, yin gaskiya ya yi nisa da mu, adalci kuwa bai iske mu ba. Muna ta neman haske, sai ga duhu, muna neman haske, sai muka yi tafiya cikin duhu.