6 Ba ku iya ganin abin da Allah ya yi mini, Ya kafa tarko don ya kama ni.
6 sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba ya kewaye ni da ragarsa.
Lokacin da suke tafiya, zan shimfiɗa musu ragata, Zan saukar da su ƙasa kamar yadda akan yi wa tsuntsun da yake tashi sama. Zan hukunta su saboda mugayen ayyukansu.
Ubangiji Allah ya ce, ‘Zan jefa taruna a kanka, a babban taron mutane, Zan jawo ka cikin taruna.
Zan yarɓa masa ragata in kama shi. Zan kai shi Babila, wato ƙasar Kaldiyawa, duk da haka ba zai gan ta ba, ko da yake zai rasu a can.
“Na rantse da Allah Mai Iko Dukka, Wanda ya ƙwace mini halaliyata, Wanda ya ɓata mini rai.
Ko na yi zunubi ina ruwanka, Kai mai ɗaure mutane? Me ya sa ka maishe ni abin bārata? Ni wani babban kaya mai nauyi ne a gare ka?
“Sa'ad da kuka ga rundunonin yaƙi sun kewaye Urushalima, sa'an nan ku tabbata ana kusan ribɗe ta.
Allah ya ɓoye musu sanin abin da zai faru nan gaba, Ya kalmashe su kowane gefe.
Kai, kun zaƙe, ku daina aikata rashin adalci, Kada ku sa mini laifi, nake da gaskiya.
Daidai ne a gare ka ka yi mugunta? Ka wulakanta abin da kai da kanka ka yi? Sa'an nan ka yi murmushi saboda dabarun mugaye?
Me ya sa kuke ɓata mini rai kamar yadda Allah ya yi? Azabar da kuka yi mini har yanzu ba ta isa ba?
Ka zama mugu a gare ni, Da ƙarfin dantsenka ka tsananta mini.
Kai kanka za ka sa mini laifi? Za ka kā da ni don kai ka barata?
Allah bai taɓa yin danniya ba, Bai kuma taɓa fāsa aikata abin da yake daidai ba.