Don lalle ne a gabatar da mu duka, a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, domin kowa yă sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko mai kyau ne, ko kuma marar kyau.
Da Dawuda ya ga mala'ika wanda yake hallakar da mutanen, sai ya ce wa Ubangiji, “Na yi laifi, na aikata mugunta, amma me waɗannan tumaki suka yi? Ina roƙonka, ka hukunta ni da gidan ubana.”