A cikin dukan abin da ya shafi hikima da ganewa wanda sarki ya nemi shawararsu, sai ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa har sau goma.
dukan mutanen da suka ga ɗaukakata da alamuna waɗanda na aikata a Masar, da kuma a jejin, suka kuwa jarraba ni har sau goma, ba su kuma yi biyayya da maganata ba,
Da Yusufu ya ga 'yan'uwansa, ya gane da su, amma ya mai da su kamar baƙi, ya yi musu magana da gautsi ya ce, “Daga ina kuka fito?” Suka ce, “Daga ƙasar Kan'ana muka zo sayen abinci.”