Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
Ga shi, zai zo a cikin gajimare, kowa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka a kansa. Wannan haka yake. Amin.
Gama yanzu kamar a madubi muke gani duhu duhu, a ranar nan kuwa za mu gani ido da ido. A yanzu sanina sama sama ne, a ranar nan kuwa zan fahimta sosai, kamar yadda aka fahimce ni sosai.