24 Ko kuwa ya zana kalmomina da kurfi a kan dutse, Ya rubuta su don su tabbata har abada!
24 a rubuta su da ƙarfe a kan dutse don su dawwama har abada!
Ubangiji ya ce, “An rubuta zunubin mutanen Yahuza da alƙalamin ƙarfe, mai bakin yakutu. An zana shi a allon zuciyarsu da a zankayen bagadansu.
Sai ku rubuta dukan kalmomin waɗannan dokoki su fita sosai bisa duwatsun nan.”
Allunan kuwa aikin Allah ne, rubutun kuma na Allah ne da ya zāna a kan allunan.
A bisa duwatsun nan goma sha biyu, sai a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila bisa ga kabilansu goma sha biyu. Za a zana sunayen kamar hatimi.
“Da ma a ce wani zai rubuta abin da nake faɗa, Ya rubuta shi a littafi!
Amma na sani akwai wani a Samaniya Wanda a ƙarshe zai zo ya tsaya mini.