“Da a ce ina da wanda zai kasa kunne gare ni, Da sai in sa hannu a kan abin da na faɗa, Allah kuwa Mai Iko Dukka ya amsa mini. “Da ƙarar da maƙiyana suke kai ni, a rubuce ne,
“Ka ɗauki takarda, ka rubuta dukan maganar da na yi maka a kan Isra'ila, da Yahuza, da dukan al'ummai, tun daga ran da na fara yi maka magana a zamanin Yosiya har ya zuwa yau.