2 “Me ya sa kuke azabta ni da maganganu?
2 “Har yaushe za ku yi ta ba ni azaba ku kuma murƙushe ni da maganganunku?
Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Mai Tsarki, Mai Gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jininmu a gun mazaunan duniya?”
Abin da ka faɗa ya iya cetonka ko ya hallaka ka, saboda haka tilas ne ka karɓi sakamakon maganarka.
Maganganun rashin tunani suke sa rauni mai zurfi kamar saran takobi, amma kalmomin mai hikima sukan warkar da raunuka.
Sukan wasa harsunansu kamar takuba, Sukan kai bāra da mugayen maganganu kamar kibau.
Ji abin da suke fada! Harsunansu suna kama da takuba a bakinsu, Duk da haka suna ta tambaya, suna cewa, “Wa zai ji mu?”
Kalmominsa sun fi mai taushi, Amma ƙiyayya tana a zuciyarsa, Kalmominsa sun fi mai sulɓi, Amma suna yanka kamar kakkaifan takobi.
An ragargaza ni da zargin maƙiyana Waɗanda suke tambayata kullum, “Ina Allahnka?”
Har yaushe za ka manta da ni, ya Ubangiji? Har abada ne? Har yaushe za ka ɓoye mini fuskarka?
“Na rantse da Allah Mai Iko Dukka, Wanda ya ƙwace mini halaliyata, Wanda ya ɓata mini rai.
“Ayuba, mutane kamarka sun taɓa yin shiru? Da ka yi ƙoƙari ka kasa kunne da mun yi magana da kai.
“Ka gama maganganunka marasa kan gado duka?
Sa'ad da ta fitine shi yau da gobe da yawan maganganunta, ta tunzura shi, sai ransa ya ɓaci kamar zai mutu.
Ayuba ya amsa.
A kowane lokaci kuna wulakanta ni, Ba kwa jin kunya yadda kuke zagina.
Ga shi kuwa, dukanku kun gani da kanku, Me ya sa kuka zama wawaye?